Yaushe Birtaniya za ta fice daga Tarayyar Turai?

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan siyasar Birtaniya sun ce suna bukatar lokaci kafin su bayyana ficewar su daga tarayyar turai.

Ana cigaba da tattaunawa a kan ta yaya da kuma yaushe Birtaniya za ta bayyana lokacin da zata fice daga kungiyar Tarayyar Turai, bayan kuri'ar raba gardama da aka gudanar a ranar Alhamis.

Kungiyar ta ce ya kamata Birtaniya ta gabatar da ficewarta a hukumance ta hanyar rubuta takarda ko kuma a cikin jawabi tun kafin a fara duk wata tattaunawa.

'Yan siyasar Birtaniya sun ce suna so a basu lokaci kafin su fara duk wani yunkuri na ficewa.

A son ransu sun fi so har sai jam'iyyar Conservative ta zabi sabon Firai minista, abin da kungiyar Tarayyar Turan ba ta yi na'am da shi ba.

A cewar ta daukar dogon lokaci wajen fitar Birtaniyan daga kungiyar, zai iya janyo ma ta cikas a yunkurin da take na ciyar da kungiyar gaba.

Sai dai kuma shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce a gaskiya bai kamata tsarin ficewar Birtaniyar ya dauki dogon lokaci ba.

''Hakan na da muhimmanci, amma ba zan yi wani fada a kan cewa ayi shi cikin gajeren lokaci ba,'' in ji Merkel.