Kungiyoyi sun kai ziyara kurkuku a Lagos

Gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ziyarar ta neman lada ce da kyautatawa fursunonin.

A Nigeria, cikin wannan wata na azumin Ramadan wasu daga kungiyoyin addini da masu fafatikar kare hakkin bil adama suna kai ziyarar bayar da tallafi a gidajen yari.

A ziyarar da kungiyar Izalatul Bid'a wa IkamatusSunnah ta kai gidajen yarin kasar da ke Ikoyi da kuma Kirikiri jami'anta sun raba kayan abinci ga mazauna gidajen yarin Msulmi da mabiya addinin Kirista.

Kungiyoyin sun ce sun dauki matakin ne domin samun lada a wannan wata mai alfarma, ba kuma tare da nuna bmnbancin addini ba.

Fursunonin da ke zaman kaso a Najeriya kan shiga wawuyacin hali sakamakon rashin abin bukatar yau da kullum, kamar sabulun wanka da na wanki da makamantan su.