Sojoji sun ceto mutane 5,000 daga BH

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun daga karshen shekarar 2015 dakarun tsaron Najeriya ke ceto mutane daga hannun Boko Haram

Dakarun runduna ta 21 ta sojojin Najeriya sun ce sun yi nasarar ceto mutane 5,000 wadanda mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su.

Wata sanarwa da ta fito daga rundunar sojin ta ce an samu damar ceto mutanen ne bayan wata fafatawa da aka yi a kauyukan Zangebe da Waiwa da Algati da kuma Mainari da ke jihar Borno.

Sanarwar, wadda daraktan yada labarai na rundunar, Sani Usman Kuka-Sheka, ya sanya wa hannu ta ce dakarun sun kashe mayakan Boko Haram shida tare da ji wa wasu dama raunuka a yayin fafatawar.

''Mun kuma samu nasarar kwato babura da kekuna daga hannun mayakan,'' in ji sanarwar.

Amma ta ce an kashe dan kato-da-gora daya tare da ji wa wani soja da dan sanda ciwo.

Kazalika, rundunar sojin ta ce ta yi arangama da wasu mayakan Boko Haram a kusa da kauyen Kusarha-Zalidava, inda ta kwace muggan makamai tare da kashe biyu daga cikinsu.