Ficewar Biritaniya ta Shafi kamfanonin Fasaha

A yanzu da Biritaniya da fice daga kungiyar tarayyar turai, kamfanonin kimiyya da fasaha na cikin tsaka mai wuya kan makomar su.

Ana sanar da ficewar Biritaniya daga tarayyar turai kamfanonin kimiyya da fasaha irin su BT, da Talk Talk, da na manhajar Sage suka sanar da hannayen jarin su ya fadi kasa warwas.

Shekaru da dama da suka gabata, Biritaniya musamman birnin London, na da tarihin irin yadda kamfanonin kimiyya da fasaha ke taka rawa wajen bunkasar tattalin arzikin su.

Daruruwan 'yan kasar ne dai suka amfana da shirin gwamnati na kimiyya da fasaha, ga misali dukkan bangarorin biyu na ma'aikata da abokan huldar kamfanonin su na da rawar da suka taka na zama a cikin tarayyar turai a wancan lokacin.

A farkon wannan shekara aka sanar da cewa kusan mutane miliyan biyu aka dauka aiki, a kamfanonin sarrafa bayanai na zamani a Biritaniya, ya yin da ma'aikatan dubu dari uku da ashirin da takwas daga cikin su suka kasance a birnin London.

Rahotonni sun bayyana cewa tattalin arzikin kamfanonin sarrafa bayanai na zamani na bunkasa cikin sauri fiye da tattalin arzikin Biritaniya baki daya.

Image caption Hannayen jarin Talk Talk sun fadi kasa warwas.

A yanzu dai wadannan kamfanoni sun fara nuna damuwa game da makomar su.