Mun kammala kwato Falluja — Sojin Iraki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sojin Iraki sun ce sun kammala kwato Fallujah

Dakarun tsaron Iraki sun ce sun kwato yanki na karshe da ke karkashin ikon mayakan IS a Fallujah.

Wani Janar din sojin kasar ya ce sojoji sun fatattaki mayakan daga wani waje da ke kusa da Golan.

Da yake magana daga yankin, Janar din ya ce hakan na nufin an kammala kwato Fallujah don hakan fadan da ake a yankin ya zo karshe.

A makon da ya gabata ma gwamnati ta yi irin wannan ikirari na cewa ta kammala kwato birnin.

Sai dai kuma hakan bai hana cigaba da gwabza fada a kan titi ba.