An sako ma'aikatan da aka sace a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya an sako wasu 'yan kasashen waje biyar da wasu 'yan Najeriyar biyu wadanda aka sace a kasar.

Wani kamfanin hako ma'adanai na Australia, McMahon Holdings, wanda mutanen ke ma aiki ya tabbatar ta cewa an sako mutanen.

An sace su ne kusa da birnin Calabar a kudu maso gabashin Najeriya a ranar Laraba.

Kamfanin ya ce ukku daga cikin ma'aikatan 'yan Australia ne, daya dan Afrika ta Kudu, daya kuma dan New Zealand -- sai kuma 'yan Najeriyar biyu.

An jima biyar daga cikinsu raunuka, biyunsu ma munana.

An dai kashe direbansu dan Najeriya.

Yankin Neja Delta, inda aka sace sun, na fama da matsalar sace mutane.

Karin bayani