Nigeria: An gurfanar da Saraki a gaban kotu

Image caption Tunda Sarki ya zama shugaban majalisar dattawa yake fama da kalubalen shari'a

A ranar Litinin ne aka gurfanar da shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki da mataimakinsa, Ike Ekeremadu, a gaban wata kotu a Abuja, a kan zargin yin dokokin jabu a majalisar.

Ministan shari'a na kasar ne dai, Abubakar Malami, ya shigar da karar.

A takardar karar, ministan na Shari'a ya zargi shugabannin biyu ne da hada kai da tsohon akawun majalisar, Salisu Maikasuwa da kuma mataimakin akawun majalisar, Ben Efeturi, wajen tsara dokokin jabu domin ba da damar zaben Sanata Bukola da Ike Ekweremadu a matsayin shugaba da mataimaki.

Tuni dai majalisar dattawan ta zargi bangaren zartarwa da bita-da-kulli.

A ranar 9 ga watan Yunin 2015 ne majalisar ta dattijai ta zabi Sanata Bukola Saraki, daga jam'iyyar APC mai mulki, a matsayin shugabanta, a inda Ike Ekweremadu wanda dan jam'iyyar adawa ta PDP ne ya zamo mataimakinsa.

An dai ce ba a gudanar da zaben ba bisa doron tsarin dokokin zauren na asali ba, a inda wasu 'yan majalisar suka yi zargin yin wasu sabbin dokokin na jabu domin samun damar darewa karagar mulkin zauren.

Hakan dai bai yi wa 'ya'yan jam'iyya mai mulki ta APC dadi ba, al'amarin da yasa aka kwashe watanni 12 ana faman sa-in-sa a kai.

Wasu daga cikin 'ya'yan jam'iyyar dai sun kai kokensu ga hukumar 'yan sandan kasar da nufin abi kadin batun.

Daga karshe rundunar 'yan sanda ta kammala bincike, daga nan kuma ofishin babban ministan Shari'a na kasar ya dora.

A makon da ya gabata ne aka kafe takardar sammace da take neman shugabannin su bayyana a gaban kotu, a farfajiyar majalisar dokokin kasar.

Lauyoyi dai na cewa, idan har an samu mutum da laifin aikata jabu a Najeriya, to hukuncinsa shi ne zaman kaso na shekaru 14.