An kai hari masallaci a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Maharan ne kawai suka mutu

A Najeriya, wasu 'yan kunar-bakin-wake da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun rasa ransu bayan da bama-bamai suka tashi da su a lokacin da suke kokarin shiga wani masallaci ranar Lahadi da daddare a birnin Maiduguri da ke jihar Borno.

Rahotanni na cewa maharan dai sun je masallacin ne da nufin shiga sahun Sallah a lokacin da jama'a suke tsaka da Sallar dare da aka fi sani da Kiyamullaili, a wani masallaci da ke Damboa Road.

Wani ganau ya shaida wa BBC cewa 'yan kunar-bakin-waken ne kawai suka mutu.

Yanzu haka dai an tsaurara matakan tsaro a kusan dukkan masallatan da ke birnin na Maiduguri.