'Yan gudun hijira na karuwanci a Borno'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan gudun hijira na cikin mawuyacin hali a Najeriya

A Najeriya, binciken da wata kungiya ta yi ya nuna cewa ana samun karuwar mata da 'yan mata da ke fadawa harkar karuwanci da wadanda ake yi wa fyade.

Binciken, wanda kungiyar Borno Development Initiative da ke tallafawa mata da rikicin Boko Haram ya shafa ta gudanar, ya nuna cewa akasarin matan na fadawa cikin wadannan mummunar sana'a ce saboda samun abin da za su biya bukatunsu na yau da kullum.

Shugabar kungiyar, Fatima Yerima Askira, ta shaida wa BBC cewa lamarin na da tayar da hankali.

A cewarta, "Akasarin matan da ke shiga karuwanci ba su wuce shekara ashirin ba, kuma suna yin haka ne domin su samu abubuwan da za su biya wa kansu bukata. Yawancin su ba sa zaune a sansanonin 'yan gudun hijira. Suna zaune ne a gidajen da aka ba su mafaka".

Sharhi - Nasidi Adamu Yahaya, Abuja

Rikicin na Boko Haram dai ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, lamarin da ya kai su ga fakewa a wurare da dama.

Baya ga batun karuwanci da fyade, wata babbar matsalar da 'yan gudun hijirar ke fuskanta ita ce matsananciyar yunwa, abin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 200 a watan jiya jiya kawai, a cewar kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta duniya.

Kazalika, ana zargin cewa jami'an da aka dora wa alhakin kula da 'yan gudun hijirar na sace abincin da ake ba su, kuma ana ganin hakan zai ta'azzara mawuyacin halin da suke ciki.