Buhari ya yi umarnin kai wa 'yan hijira agaji

Image caption Shugaba Buhari ya ce yana cikin damuwar halin da 'yan gudun hijira suka samu kansu a ciki

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin a kafa wata tawagar kai agajin gaggawa ga dubban 'yan gudun hijirar da ke fama da rashin isasshen abinci a yankin arewa maso gabashin kasar.

Ministan Lafiya, Farfesa Isaac Adewale, shi ne ya sanar da kafa tawagar, yayin wani taron gaggawa da kungiyoyin bayar da agaji na kasashe suka ranar Litinin a Abuja, babban birnin Najeriyar.

Ya ce, ''Shugaban kasa ya matukar damuwa da wannan lamari, ya kuma bukace mu kafa kwamitin da zai kai daukin gaggawa, irin wanda aka kafa lokacin yaki da cutar Ebola. Don haka a karshen taron nan za mu tsara yadda za a kafa kwamitin, sannan mu gabatar da tsarin ga shugaban kasa a ranar Talata.''

Farfesa Adewale ya kara da cewa ma'aikatar lafiya za ta kai wa yara dubu 200 masu fama da tamowa agaji, amma sabon nazarin da aka yi ya nuna dole a ninka agajin.

''Yanzu muna shirya yadda za mu kula da yara dubu 600 ne da ake fama da matsananciyar yunwa, za mu kai musu duk abubuwan da ake bukata kamar ruwa da abinci na musamman wadanda aka hada domin ceto su daga yiwuwar mutuwa,'' in ji ministan.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban mutane ne da suka hada da yara ne ke cikin halin ha'ula'i na yunwa

Ita kuma shugabar kungiyar AOA Global mai mazauni a Amurka, Dr. Ayoade Alakija, wadda ta kira taron gaggawar, ta ce, wani sabon kiyasin da suka yi ya nuna cewa a wannan watan na Yuni, yara akalla biyar na mutuwa a kusan kowace sa'a a arewa maso gabashin Najeriyar.

Sauran kungiyoyin da suka halarci taron na gaggawa sun hada da hukumomin raya kasashe na Burtaniya da Amurka, DFID da USAID, da na Tarayyar Turai, da kuma hukumomin Majalisar Dinkin Duniya masu kula da kananan yara da 'yan gudun hijira.

A kwanan nan ne wani rahoto na kungiyar agajin likitocin Medecins Sans Frontieres ya ce, kimanin mutane 200 sun mutu da yunwa a garin Bama, na jihar Borno, a watan da ya wuce.