Turai za ta yi taro kan Biritaniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Manyan kasashen Turai sun bukaci Biritaniya ta gaggauta ficewa daga Tarayyar Turai

Manyan kasashen Turai za su yi taro a kan ficewar Biritaniya da Tarayyar Turai.

Shugabannin kasashen Jamus da Faransa da Italiya na ganawa a birnin Berlin kan yadda za a gaggauta fitar da Biritaniya daga Tarayyar ta Turai.

Ministan kudi na Biritaniya George Osborne ya gabatar da wani jawabi, inda ya yi kokarin kwantar da hankulan mutanen da ke ganin tattalin arzikin kasar zai fada mawuyacin hali, yana mai cewa tattalin arzikin na nan da karfinsa.

Hannayen jarin Biritaniya na ci gaba da tangal-tangal, yayin da kudin kasar, Fam, ya ci gaba da faduwa idan aka kwatanta da Dala.