An bayar da belin Saraki da Ekweremadu

Image caption Wannan dai ita ce shari'a ta biyu da Saraki ke fuskanta a kotunan Najeriya

Wata babbar kotu a Abuja, babban birnin Najeriya ta bayar da belin shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu.

Alkalin kotun Yusuf Haliru, ya ce ya bayar da wannan beli ne domin hakan ya bai wa mutanen da ake zargi damar fuskantar shari'a.

Ya kuma kara da cewa an bayar da belinsu ne bisa kimar da suke da ita, ganin irin manyan mukaman da suke rike da su.

A cewarsa ba a samu wadanda ake tuhumar da laifi ba, don haka akwai bukatar bayar da belinsu.

Sai dai alkalin ya bayar da umarni cewa dole wadanda ake tuhumar suka gabatar da mutanen da za su tsaya musu guda biyu wadanda kuma suka mallaki kadara a Abuja.

''Rashin yin hakan zai sa a kai su gidan yari na Kuje da ke babban birnin kasar,'' in ji mai shari'a Haliru.

'Karin bayani kan shari'ar'

Sai dai tun kafin alkalin ya bayar da belin wadanda ake tuhumar, lauya mai kare Sanata Saraki ya nemi kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa saboda kimar da yake da ita.

Lauya Paul Erokoro ya ce, ''Shi ne fa shugaban majalisar dattawan kasar nan, ina zai gudu ya je? Ai kimarsa ta wuce haka. Don haka ina rokon alfarmar mai shari'a da da ya bayar da belinsa ko don alfarmar kujerarsa.''

A karshe lauya mai shigar da kara Muhammadu Diri, ya ce kotu na iya bayar da belin Saraki amma ya soki bayar da belin sauran wadanda ake tuhuma.

Sanata Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu da tsohon akawun majalisar dokokin kasar Salisu Mai-Kasuwa na fuskantar tuhuma ne kan yin dokokin jabu a majalisar dattawan kasar.

Kotun ta dage sauraron karar har zuwa 11 ga watan Yuli.