Kura ta ciji wani yaro a Afirka ta kudu

Hakkin mallakar hoto chris gomersall alamy
Image caption Kurar ta yi sanÉ—a ne ta shiga tantin da yaron ke ciki

Kura ta ciji wani yaro dan shekara 15 a lokacin da yake bacci a wani tanti da ke gandun dajin Kruger National Park na kasar Afirka ta kudu.

Kafafen watsa labaran kasar sun ambato jami'an gandun dajin na cewa yaron ya farka ne kawai ya ga kurar ta hau mukamikinsa, sannan ta ja rigarsa kafin ta hau kansa.

Wani kamfanin dillacin labarai kan dabbobi na kasar, SANParks, ya ce an garzaya da yaron asibiti, inda aka ba shi magani.

Da alama kurar ta shiga cikin tantin ne ta wani rami.