Kenya: Dalibai sun kona dakunan kwanansu

Image caption Lamarin dai ya sa fiye da dalibai 800 sun kwana a cikin sanyi

Hukumomi a kasar Kenya sun ce dole daliban da suka kona dakunan kwanansu bayan an hana su kallon wasan kwallo su biya tara.

A ranar Asabar ne dai daliban na makarantar sakandaren Itierio da ke yammacin kasar suka kona dakunan kwanan nasu bayan an gaya musu cewa ba za a bar su su kalli wasan da aka yi tsakanin Croatia da Portugal na gasar cin kofin Turai ba.

Wata majiya ta 'yan sanda ta ce daliban sun yi amfani da fetur din da aka yi satar shigar da shi makarantar domin kona dakunan barcin.

Lamarin dai ya sa fiye da dalibai 800 sun kwana a cikin sanyi.

Kawo yanzu dai ba iya kiyasta asarar da lamarin ya janyo ba, amma shugaban makarantar ya ce asarar za ta kai ta daruruwan miliyoyin kudin kasar, wato shillings ne.

Duk da cewa ba a san takamaimai abin da ke dugunzuma daliban ba, masu sa ido na danganta hakan da rashin daukar matakan ladabtarwa kan daliban, da lalacewar dangantaka tsakanin dalibai da malamai.

Ko a makon jiya, shugaban kenya Uhuru Kenyata ya umurci malamai da su samar da kyakyawar danagantaka tsakanin su da dalibai domin kaucewa ire iren wadannan matsaloli.