Dakarun Chadi sun kai dauki Nijar

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Issoufou ne ya nemi takwaransa na Chadi ya taimaka masa da dakaru

Rahotanni daga yankin jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar na cewa sojojin Chadi sun soma isa kasar, domin kai wa takwarorinsu na Nijar din dauki dangane da yakin da suke yi da 'yan Boko Haram.

A yanzu haka dai ayari na farko na sojojin Chadin na cikin kasar ta Nijar kuma za su fara aiki ne ba bata lokaci.

Hukumomin kasar sun tabbatar da zuwan dakarun Chadin amma ba su fadi adadin su ba.

Sai dai tun da farko rahotanni sun ce kimanin dakaru 2,000 ne Chadi za ta tura Nijar.

Wani mai sharhi kan al'amuran tsaro Farfesa Issoufou Yahya na jami'ar Abdou Mumini ta Yamai, ya shaida wa BBC cewa zuwan dakarun Chadin na iya yin tasiri wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

''Zuwansu zai taimaka sosai saboda Chadi suna da kayan yaki ba na wasa ba, don haka za su taimaka kwarai,'' in ji Farfesan.

A ranar 3 ga watan Yuni ne mayakan Boko Haram suka kai wani mummunan hari garin Bosso wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Nijar 24 da na Najeriya biyu da kuma jikkata wasu 111.

Wannan lamari ne yasa shugaban Nijar Muhammadou Issoufou ya je Chadi inda ya gana da takwaransa Idris Deby, ya kuma nemi ya taimaka masa da sojoji domin tunkarar 'yan kungiyar Boko Haram, saboda yadda suke zafafa hare-hare a baya-bayan nan.

Kungiyoyin adawar kasar ma dai sun yi maraba da zuwan dakarun Chadin, amma sun yi gargadi da cewa gwamnati ta yi hattara ta bi a hankali.