Kano: Teloli sun koka kan rashin dinki a bana

Image caption Matsin tattalin arziki a Najeriya na shafar masu kananan sana'o'i

A Najeriya, bisa ga dukkan alamu matsalolin tattalin arziki sun shafi shirye-shiryen Sallar azumi, inda wasu teloli suke koka wa kan raguwar masu kai musu dinki a bana.

A irin wannan lokaci dai jama'a kan dinka sababbin kaya tare da iyalansu domin shan shagalin bukukuwan Sallah.

Sai dai bisa ga dukkan alamu bana hantsi ya dubi ludayi.

Wani tela a Kano mai suna Rabi'u Hashim Fagge, ya shaida wa BBC cewa bana abin sai godiyar Allah.

A cewarsa, "Ba ma samun mutanen da ke kawo dinkuna domin cin bukukuwan Sallah da ke tafe. Da an yi Sallar Asham za ka ga teloli sun rufe shagunansu sun tafi gida, ba kamar yadda a baya muke kwana a shaguna muna aiki ba."

Rabi'u ya ce matsin tattalin arziki da rashin kudi a hannun mutane, da tsadar kaya sun sanya mutane hakura da dinka tufafi.