Umrah ta gagari wasu 'yan Nigeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Miliyoyin 'yan Najeriya ke zuwa Umrah kowacce shekara amma bana abin ya gagara

Tashin gwauron-zabin da farashin tikitin jirgin sama daga Najeriya zuwa Saudiyya don Umrah a wannan lokaci ya yi, ya sanya maniyyata da dama gaza zuwa kasa mai tsarki.

Dimbin 'yan Nijeriya ne duk shekara suke tururuwa zuwa kasar Saudiyya a irin wannan lokaci, musamman domin samun dace da daren Lailatul Qadari.

Sai dai a wannan karon, matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar ba zai bai wa maniyyata masu yawa damar zuwa kasar ba.

Sharhi, Mukhtari Adamu Bawa, BBC Hausa daga Kano.

A bana matsin rayuwar da ake ciki ta sa mutane da dama da suka saba zuwa kasar Saudiyya duk shekara domin yin Umrah sun yanke kauna, kamar irin su Sani Ali Na'iya.

Sai dai akwai dimbin maniyyatan da har yanzu ke fadi-tashin dagawa zuwa Saudiyya inda wasu ke lale kudi har sama da Naira dubu 200 domin sayen biza, amma tikitin zuwa ya gagara.

Wani mai kamfanin shirya tafiya zuwa Umrah daga Kano, Rabi'u Ahmad Muhammad, ya ce a bana kimanin kashi 35 zuwa 40 cikin 100 na abokan huldar da suka saba shirya wa tafiya umrah ne suka fasa zuwa wannan ibada.

Da yawan maniyyatan dai sun fasa wannan tafiya ne saboda tsadar tikiti da na guzuri da kuma la'akari da tashin farashin kayan bukatun rayuwa da ya kamata a bar wa iyali kafin a kama hanya.

Raguwar masu tafiya umrah daga Nijeriya wata manuniya ce kan yadda matsalar hauhawar farashi a kasar ke shafar ba kawai rayuwar mutane ba, har ma da ayyukan ibada da Musulmi ke matukar bege.