Fafaroma na so a nemi afuwar 'yan luwadi

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Paparoma ya fadi hakan ne a cikin jirgi kan hanyarsa ta dawowa daga Armenia

Fafaroma Francis ya ce akwai bukatar Cocin Roman Katolika ta nemi afuwar 'yan luwadi a kan musguna musu da take yi.

Fafaroma Francis ya ce akwai bukatar Cocin Roman Katolika ta nemi afuwar 'yan luwadi a kan yadda abubuwan da ta dinga yi musu.

Ya ce kotun ba ta da hurumin da za ta ladabtar da 'yan luwadi, kuma ya kamata ta girmama su.

Fafaroman ya shaida wa manema labari wannan batu ne yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Armenia.

Badakalar lalata da yara a cocin Katolika Shugabannin Cocin Katolika da na Orthodox sun gana

Ya ce baya ga haka kuma akwai bukatar cocin ya nemi afuwar mata da marasa galihu da yara da ake tursasu aikin karfi.

'Yan luwadi da dama dai sun yabi tare da jinjinawa Fafaroma Francis kasancewar zamowarsa Fafaroman da ya fi tausayi a tarihin baya-bayan nan.

Amma masu tsaurin ra'ayi daga darikar katolika sun soke shi kan wadannan kalamai nasa, inda suka ce masu tsauri ne.