An kulle Nenadi da Femi Kayode a gidan yari

Hakkin mallakar hoto AS Aruwa
Image caption Femi Fani Kayode ya kasance wani jagora lokacin yakin neman zaben Goodluck Jonathan a 2015

Alkalin wata babbar kotun tarayya da ke Lagos a kudancin Najeriya, ya bukaci a kai tsohuwar ministar kudi Nenadi Usman, da Femi-Fani Kayode gidan yari bisa zargin sace kudin gwamnati.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ce dai ta gurfanar da su a kotun, tana zarginsu da laifuka 17.

Laifukan sun hada da sata, da hada baki domin yin satar da karkatar da kudin gwamnati kimanin naira biliyan 4.9 wajen yin harkokin siyasa.

Mutanen dai sun musanta zargin da ake yi musu, lamarin da yasa alkalin, mai shari'a M.S. Hassan ya bayar da umarnin rufe su kafin ranar daya ga watan Yuni domin ci gaba da shari'a.

Nenadi Usman da Femi Fani-Kayode dai sun taka rawa wajen yakin neman zaben tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, wanda bai yi nasara ba.

Misis Nenadi dai ita ce daraktar kudi ta kwamitin yakin neman zaben Mista Jonathan yayin da shi kuma Mista Kayode shi ne sakataren watsa labarai ne kwamitin.