An sace wani mawakin siyasa a Adamawa

Image caption Iyalan Ado sun ce rabonsu da ganinsa tun ranar Juma'a da safe

'Yansanda a jihar Adamawan Najeriya sun tabbatar da bacewar wani fitaccen mawakin Hausa da aka daina ganinsa jim kadan bayan ya fitar wata sabuwar waka da ke Allah-wadai da halayen wasu 'yan siyasa a jihar.

Iyalan mawakin Ado Halliru Daukaka, sun shaida wa BBC cewa sun yi masa gani na karshe ne da safiyar ranar Jumu'a, kuma har yanzu ba su da labarinsa.

Matarsa Malama Hadiza Dauda ta ce ya fita da zummar zai je shagonsa, amma tun lokacin bai koma gida ba.

Malama Hadiza ta ce, ''Tun daga lokacin muka yi ta kokarin nemansa a waya amma shiru ka ke ji har inda nan ke motsi.''

Ta ce a iya saninta maigidanta ba shi da abokin gaba, amma bata sani ba ko wani ke bin sa da mugun nufi.

Tuni dai masoyansa ma suka fara alakanta bacewarsa da fitowar sabuwar wakar tasa mai taken, ''Gyara kayanka.''

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce tana iya bakin kokarinta wajen ganin an gano inda yake.

Wannan mawaki dai ya dan jima yana haskawa a jihar Adamawa sakamakon wakokin siyasa da yake yawan yi.