Shin ko sharar malalar mai za ta yi nasara?

Hakkin mallakar hoto Abdullahi Kaura
Image caption Halin da wasu yankunan Niger Delta ke ciki kenan

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani gagarumin shiri da ba a taba yin irinsa ba na kashe kimanin dala biliyan daya domin share malalar mai a yankin Niger Delta. Kuma kamfanonin mai da suke jawo wannan malala ne za su biya wannan makudan kudi. Amma abin tambayar shi ne, ko hakan zai tasiri?

Wakilin BBC Abdullahi Kaura Abubakar ya kai ziyarar gani da ido zuwa yankin, inda ya ce duk da dumbin arzikin da ke yankin Niger Delta, amma babu wani cigaba da suka samu sai matukar koma baya.

Ya ce sun ratsa ta wani jeji da ke da dumbin albarkatu iri-iri, amma babu halin mazauna wajen su more shi.

Wani mai fafutukar kare muhalli wanda ya girma a yankin, Erabanabari Kobah, ya shaida wa BBC cewa, ''Wannan jeji cike yake da albarkatu amma saboda malalar mai da ke ta aukuwa jejin ya mutu, har ta kai ba shi da wani amfani. Mutane ba sa iya yin su a cikin wannan kogin a yanzu. Abin bakin ciki ne matuka ganin yadda hakan ya kasance.''

Gonar wata mata mai suna Comfort Gbode, na dab da wata tashar man kamfanin Shell wadda ta samu matsala ta zubar da mai a shekarar 2012, lamarin da ya bata mata gonar.

Ta shaida wa wakilin BBC cewa kamfanin Shell ya yi kokarin gyara gonar amma ba a yi aikin da kyau ba.

''Na ga motoci sun zo da kasa daga wasu wuraren, wai sun zo gyaran gonar amma har yanzu ba ma iya noma a wurin,'' a cewar Misis Comfort.

Sai dai kuma kamfanin Shell na cewa da zarar an samu matsalar malalar mai, ya kan gaggauta tura ma'aikata wurin domin tsayar da malalar da kuma tabbatar da cewa malalar ba ta yi barna ba sosai.

Ministan muhalli ta Najeriya Amina Mohammed, ta bayar da tabbacin cewa lallai a wannan karon za a yi aikin da kowa zai yi na'am da shi.

A hirarta da Abdullahi Kaura, Ministar ta ce, ''Shakku da ake nunawa a yanzu shi ne ko za a yi wannan aiki da gaskiya da kuma adalci. Ba batun raba kudi bane. Batun samo mutane ne da za su yi aikin da ya kamata domin gyara muhallin yankin Naija Delta. Kuma abin da hakan yake nufi shi ne yadda za a koya wa su 'yan yankin Ogonin yadda za su yi aikin da kansu.''

Hakkin mallakar hoto Abdullahi Kaura
Image caption Koguna na mutuwa ta yadda masunta ba sa iya kamun kifi a ciki

'Kalubale'

Babban kalubale dai a yanzu wajen aiwatar da wannan aiki shi ne shawo kan al'ummar da malalar man ta shafa da ta amince da aikin sharar.

Adullahi Kaura ya cigaba da cewa, da ka bar gabar ruwa za ka tarar da Bodo, wanda gari ne na masunta kuma ya yi fice a shekarar da ta wuce bayan kamfanin Shell ya biya al'ummar wajen diyy mai dumbin yawa ta barnar da malalar mai ta jawo musu.

'Tashin tashina kan batun masu gidan rana'

A wata sasantawa da ba a taba irinta ba a baya, an raba wa dubban mutanen Bodo kudin diyyar bata musu muhalli, inda kowannensu ya samu kusan dalar Amurka dubu uku. Sai dai wannan kudin ya jawo rarrabuwar kawuna tsakanin al'ummar.

Cikin yarjeniyoyin da aka cimma akwai cewa tilas ne kamfanin Shell ya gyara barnar da malalar man ta haifar.

Sittu Emmanuel na daya daga cikin wadanda suka amfana da kudin, "Ni dai bana goyon bayan share malalar man. Abin da nake so shi ne kudi, nafi son a bai wa al'ummarmu kudin da za'ayi aikin dashi," in ji shi.

Amma ba Sittu Emmanuel ne kadai ba ya son a share malalar man ba, kashi 80 cikin 100 na talakawan wannan yanki na cewa ba sa bukatar sharar malalar man, abin da suke so kawai shi ne a raba masu kudin aikin.

'Sasantawa'

Image caption Yawancin 'yan al'ummar Bodo sun gina sabbin gidaje da kudin diyyar da aka biya su

Shugaban majami'ar Katolika da ke Bodo, Father Abel Agbulu, shi ne ya shiga tsakani ya sasanta su bayan fada ya barke tsakanin mutanen Bodon, abin da ya kai ga kashe mutum hudu.

Father Abel ya ce, ''Bari in gaya ma abin da yasa suka gwammace a basu kudin, babu yarda a tsakanin su ne. Mutanen basu yarda da wakilansu da ke tattaunawa kan batun ba. Bayan haka kuma ana fama da kuncin rayuwa.''

An dai shafe shekara uku kenan ana tattaunawa kan wannan aikin amma har yanzu ba a kai ga samun maslaha ba tukunna.

Jakadan kasar Holland a Najeriya John Groffen, yana daya daga cikin wadanda ke shiga tsakani domin warware matsalar.

''Muna kokarin ganin an gudanar da aikin ne ba tare da magudi ba kamar yadda aka sha yi a baya, inda ake bai wa'yan kwangila aiki ba tare da bin tsari da doka ba. Shi yasa wasu 'yan kwangilar da matasa ke ganin za a yi ban dasu, wannan ne ya sa suke tayar da jijiyar wuya,'' in ji Mista Groffen.

Kafin a warware sarkakkiya dangane da kwangilar, akwai yiwuwar yankin zai cigaba da gurbacewa.

Bodo dai daya ne kawai daga cikin garuruwan da ke fama da gurbacewar muhalli, da akwai daruruwa irinsa a yankin Niger Delta.

Aikin share malalar man dai na da girman gaske, zai iya daukar tsawon shekara 25 kafin a kammala shi.

To amma ko yaya gwamnati za ta cimma nasarar yin wannan aiki cikin kwanciyar rai da kuma amincewar al'ummar yankin? Ganin irin yadda masu tayar da kayar baya a yankin yanzu haka ke takun-saka da gwamnati.