Mutum 45 ne suka mutu a Sudan ta kudu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana takun-saka tsakanin Salva Kiir da Riek Machar

A Sudan ta Kudu, akalla mutum 45 ne aka tabbatar sun hallaka, dubbai kuma sun bar gidajensu sakamakon fadan da ya barke a karshen makon jiya a jihar Wau da ke arewa maso yammacin kasar.

An ce tashin hankalin ya barke ne a ranar Juma'a, bayan shugaba Salva Kiir ya kori gwamnan sabuwar jihar, ya kuma maye gurbinsa da wani.

Sakataren majalisar dinkin duniya, Ban Ki-Moon, ya yi kira ga masu fadan da su bari a isar da kayan agaji ga masu bukata.

Tun bayan karbar 'yancin kai shekara biyar da suka gabata, Sudan ta kudu ta fada rikicin siyasa bayan da shugaba Kiir ya tsige mataimakinsa Riek Machar.

Lamarin da ya janyo asarar rayuka da sanya miliyoyin mutane tserewa daga muhallansu.

A karshen mako ma fadar gwamnatin kasar ta sanar da cewa ba za ta gudanar da bukukuwan cikar shekara biyar da samun 'yancin kai ba, saboda matsalar rashin kudi.

Amma wasu na danganta hakan da zaman doya da manjar da ake yi tsakanin Mista Kiir da Machar tun bayan mayar da shi kan mukamin sa wata da suka gabata.