'Karta na maganin shanyewar ɓarin-jiki'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Karta na cikin wasannin da mutane suka fi yi

Masu binciken kimiyya a kasar Canada sun ce masu cutar shanyewar ɓarin-jiki ka iya samun sauki cikin gaggawa idan suka yin wasannin da suka hada da karta.

Sun ce sun gano cewa wasan karta yana kara karfin gabobin masu fama da cutar.

Masu binciken na sake yin nazari a kan wasannin da suka kamata masu cutar shanyewar bari- jiki su rika yi da nufin samun waraka, da kuma duba yiwuwar ko wasannin karta da na gargajiya sun fi gashin da ake yi wa gabobinsu saurin kawo waraka.

An kuma gano cewa yawan motsa hannaye da kafada a lokacin wasan karta na inganta lafiyar masu cutar.

Labarai masu alaka