Al'ummar Zamfara na rayuwa cikin tsoro

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army
Image caption Al'ummar kauyukan Zamfara dai sun ce suna fuskantar hare-hare

Rahotanni daga jihar Zamfara a arewacin Najeriya na cewa, 'yan fashin da suka addabi jihar sun sauya salon hare-haren da suke kai wa al'umma.

Wasu da suka zanta da BBC sun ce sabon salon da 'yan fashin shanun suka fito da shi shi ne na tsare 'yan kasuwa a manyan hanyoyi suna kwace musu kadarorinsu.

Mazauna yankunan karkara wadanda su ne abin ya shafa na cigaba da kokawa da halin rashin tsaro da ke addabar yankunansu, inda suka ce a yanzu haka suna rayuwa ne cikin tsoro da fargaba.

Kazalika al'ummar yankunan sun ce 'yan fashin sun hana manoma rawar gaban hantsi a bana, ta yadda suke shiga gonaki suna kashe manoma.

'Yan sanda a jihar dai sun tabbatar da hakan na faruwa, amma sun ce suna daukar matakan dakile aikace-aikacen 'yan fashin.

An kashe mutane a Zamfara

Sharhi daga Haruna Shehu Tangaza, BBC Hausa daga Abuja

Manoma basu da damar zuwa gonakinsu musamman idan gona ta yi nisan kilomita biyar daga gari.

Image caption A can baya ma an taba kashe gomman mutane a lokaci guda a jihar ta Zamfara

Mazauna yankin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro suna bakin kokarinsu sai dai sabbin dabarun da 'yan fashin suka bullo da su, na kara jefa jama'a cikin tashin hankali.

Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya ya fitar da sanarwa a ranar Talata, yana cewa sojoji sun kai samame kan sansanoni daban-daban na 'yan fashin da ke kauyen Rikwa na jihar, inda suka fatattake su tare da kwato makamai da kuma dabbobi fiye da 500.

'Yan fashin sun kwashe kusan shekara takwas suna fashin shanu da kashe mutane tare da sace dabbobinsu.