An kai harin kunar-bakin-wake a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jam'ian tsaron Afghanistan na fama da hare-haren 'yan Taliban

Jami'ai a kasar Afghanistan sun ce wani dan kunar-bakin-wake ya kai wa ayarin motocin 'yan sanda hari a Kabul, babban birnin kasar inda ya kashe 'yan sanda 40.

Ya jefa bama bamai biyu a kan ayarin motocin da ke dauke da sababbin kananan hafsoshin 'yan sanda wadanda ke kan hanyarsu ta komawa bariki daga bikin yaye su.

Gwamnan lardin Paghman Haji Mohammad Musa Khan ya shaida wa BBC cewa mutane da dama sun jikkata.

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin, da ma harin da aka kai kan wata motar bas a makon jiya, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 14.

'Yan kasar Nepal da ke aiki a matsayin jami'an tsaron ofishin jakadancin Canada na cikin wadanda suka mutu.