Fitaccen marubuci Elechi Amadi ya mutu

Hakkin mallakar hoto HEINEMANN
Image caption Littafin, wanda aka wallafa a shekarar 1966, ya karbu sosai a kasashen Afirka

Fitaccen marubucin nan dan Najeriya Elechi Amadi ya mutu yana da shekara 82.

Amadi ya mutu ne a wani asibiti da ke birnin Fatakwal da ke jihar Ribas, sai dai ba a bayyana cutar da ta yi sanadin mutuwarsa ba.

Marubucin ya shahara ne saboda littafin da ya rubuta mai suna The Concubine, wanda ya yi bayani kan aure da al'adun da aka haramta wajen yin sa.

Littafin, wanda aka wallafa a shekarar 1966, ya karbu sosai a kasashen Afirka.

Sauran litattafan da ya rubuta su ne: Sunset in Biafra, Peppersoup, The Slave da kuma The Road to Ibadan.

Amadi, wanda ya yi Digirinsa a ilimin koyar da kimiyya na physics da lissafi a Jami'ar Ibadan, ya shiga rundunar sojin Najeriya, kuma ya ci gaba da yin aiki da ita har lokacin da aka yi yakin-basasa, duk kuwa da cewa shi dan Niger Delta ne, yankin da ke cikin yankunan da ke son kafa Jamhuriyar Biafra a wancan lokacin.