Ministan Shari'a bai amsa kiran majalisa ba

Image caption A ranar Litinin ne dai aka gurfanar da shugaban majalisar dattawan Najeriyar, Sanata Bukola Saraki da mataimakinsa, Ike Ekeremadu

A ranar Alhamis ne majalisar dattawan Najeriya ta kori wani mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin shigar da kara daga harabar majalisar.

Mista Okoi Obla dai ya je majalisar ne a matsayin wanda ministan shari'a na kasar Abubakar Malami, ya tura domin ya wakilce shi a zuwan da ya kamata ministan ya yi a ranar Alhamis, a gaban kwamitin majalisar da ke kula da harkokin shari'a da kare hakkin dan adam.

Majalisar dattawan dai ta gayyaci ministan shari'ar ne domin yi mata bayani kan karar da ya shigar kan shugabanta da mataimakinsa gaban kotu.

Sai dai wakilin ministan shari'ar bai shaida wa majalisar dalilin rashin zuwansa da kansa ba.

A ranar Litinin ne dai aka gurfanar da shugaban majalisar dattawan Najeriyar, Sanata Bukola Saraki da mataimakinsa, Ike Ekeremadu, a gaban wata kotu a Abuja, a kan zargin yin dokokin jabu a majalisar.