Tsohon Sakataren PDP Ojo Madueke ya mutu

Image caption Madueke ya dade cikin harkokin siyasar Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa tsohon ministan harkokin wajen kasar kuma jigo a jam'iyyar PDP, Cif Ojo Madueke ya mutu.

Wasu majiyoyi dai sun ce Mista Madueke ya mutu ne a wani asibi da ke Abuja, babban birnin kasar ranar Laraba da almuru.

Sun kara da cewa tsohon Sakataren jam'iyyar ta PDP ya kamu da rashin lafiya ne a cikin jirgin da ya dauko shi daga Dubai zuwa Abuja bayan ya baro Amurka, kuma da saukar jirgin aka garzaya da shi asibiti.

Sai dai marigayin ya mutu ne jim kadan bayan an kai shi asibitin.

Cif Madueke ya rike mukamai da dama a Najeriya da kasashen waje.

Tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya nada shi Maduekwe a matsayin minsitan al'adu da yawon bude idanu a shekarar 1999, yayin da ya zama ministan sufuri a shekarar 2001.

A lokacin ya rika yin shelar ganin 'yan kasar sun koma hawa kekuna kasancewarsa mutum mai sha'awar hawa keke.

Sai dai ya sha suka daga wajen 'yan kasar wadanda ke ganin ya kamata a gyara hanyoyi tukunna.

An haifi Mista Madueke ne a ranar shida ga watan Mayu na shekarar 1945 a jihar Abia da ke kudancin Najeriya.