Ana zaben shugaban kasa a Australia

Hakkin mallakar hoto Reuters

Al'umomin kasar Australia na kada kuri'a a zaben shugaban kasa.

Bayan kada tasa kuri'ar, Firayim Ministan kasar, Malcolm Turnbull, wanda dan jam'iyyar Liberal Party ne, ya ce wannan ne lokaci mafi dacewa don daidaita al'amura a kasar.

Mista Turnbull ya sha alwashin rage kudin haraji ga manyan 'yan kasuwa da nufin bunkasa tattalin zarkin kasar, tare da samar da aikin yi.

A bangare guda kuma, abokin hamayyarsa na jam'iyyar Labour, Bill Shorten ya yi alkwarin kara kudin haraji domin gwamnati ta samu kudaden da za ta raya makarantu da asibitocin kasar.