Bangladesh: Sojojin kundumbala sun afkawa gidan shayi

A kasar Bangladesh, ga alama an tasam ma kammala wani gagarumin aikin ceto a Dhaka, babban birnin kasar, bayan sojojin kundumbala sun abka wani gidan shayi, inda wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da jama'a.

An samu akalla gawakin mutum biyar, bayan jami'an tsaro sun bankade ko'ina a gidan shayin.

Kazalika an halaka 'yan sanda biyu a dauki-ba-dadin.

'yan sanda sun ce an ceto mutum 12 daga cikin wadanda ake yi garkuwa da su, ciki har da mutum hudu wadanda ba 'yan kasar ba, biyu daga ciki 'yan kasar Sirilanka ne, wadanda 'yan sanda suka ce ba a musu ko kwarzane ba.

Akwai mutanen Italiya masu yawa a cikin wadanda aka yi garkuwa da su din, kodayake an ce watakila da Japanawa cikin su.

Kungiyar IS ta yi ikirarin cewa mayakanta ne suka kai harin.