An yi jana'izar mutanen da mota ta kashe a Bauchi

A Najeriya, an yi jana'izar ma'aikatan tsaro su 11 da kuma direban wata babbar motar dakon kaya wadanda suka rasa rayukansu a wani mummunan hadarin mota a jihar Bauchi.

Hadarin dai ya faru ne ranar Alhamis da maraice yayin da ma'aikatan tsaron ke komawa garin Bauchi daga yankin Ningi inda suka ta fi aikin sintiri, inda a kan hanya motarsu da wata tanka suka yi taho-mu-gama.

An dai yi Sallar jana'izar ma'aikatan tsaron na Dangan Security ne a Masallacin Gwallaga da ke birnin Bauchi, daga nan kuma sai aka kai gawawwakin mutanen goma sha biyu makabarta, inda aka binne su, kowa da kabarinsa, amma an jera su wuri guda. Shugaban rundunar tsaro ta Danga Security, wadda ta rasa jami'anta goma sha daya a hadarin motar, Alhaji Yusufu Hassan, ya ce al'amrin ya girgiza su.

Wannan hadarin mota dai, ya jefa kusan illahirin jihar ta Bauchi cikin jimani alhini, inda kusan a wurare da dama, babu hirar da ake yi illa ta mutuwar da kuma munin hadarin, yayin da jama'a ke ci gab ad tururuwa zuwa gidajen 'yan uwa da abakn arzikin mamatan domin ta'aziyya.