Za mu sake gina Niger Delta — Buhari

Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta sake gina kasar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta sake gina kasar, ciki har da yankin Naija Delta.

Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da ya gana da wakilan yankin na Naija Delta wadanda babban Basaraken gargajiyar yankin Alfred Diette-Spiff, ya jogoranta zuwa fadar shugaban kasa ranar Alhamis.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, "Mun yi niyyar sake gina Najeriya ta yadda 'ya'yanmu da jikokinmu za su samu kasar da za su iya zama a cikinta. An lalata kasar nan sosai, don haka ina so ku gaya wa mutane su yi hakuri."

Shugaban na Najeriya ya ce gwamnatinsa na duba tsare-tsaren da gwamnatin marigayi Shugaban kasar Umaru Musa 'Yar Adua ta yi domin ci gaban yankin domin ganin inda ta tsaya da zummar dorawa.