MDD ta nemi a saki tsohon minista a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaro sun tsare Marafa Hamidou Yaya a watan Afrilun shekarar 2012

Majalisar dinkin duniya ta bukaci gwamnatin Kamaru ta sake tsohon Minista Marafa Hamidou Yaya wanda take zargin an tsare shi a gidan yari ba gaira ba dalili.

Haka kuma majalisar ta bukaci a biya shi diyya.

Majalisar ta bayyana haka ne bayan wani taron da wakilanta daga sassan duniya suka yi, taron da Kamaru ba ta aika wakilinta ba.

Jami'an tsaro sun tsare Marafa Hamidou Yaya a watan Afrilun shekarar 2012, sa'annan kuma suka mika shi ga kotu ta musamman mai shari'a a kan manyan laifuffuka, wadda ta daure shi na tsawon shekaru 25 a watan Satumban 2012.

Kotun ta ce ta same shi da hadin baki wurin wawure kudade CFA biliyan 24 ($m31).

Bayan daukaka karar da lauyansa ya yi ne kotun koli ta rage hukuncin zuwa shekaru 20.

A yanzu haka dai gwamnatin Kamaru ba ta ce komai ba game da bukatar da majalisar dinkin duniyar ta yi.