Zika ta bulla a Guinea-Bissau

Hakkin mallakar hoto Roger Eritja
Image caption Mutum uku ne suka kamu da cutar ta Zika a Guinea Bissau

Mahukunta a kasar Guinea-Bissau sun tabbatar da cewa a karon farko an samu mutum uku da suka harbu da cutar Zika a kasar.

Sun ce an samu mutanen da suka harbu da cutar ne a wasu tsibirai da ke Bijagos Archipelago da ke kudancin kasar.

A cewar mahukuntan, tuni an kafa wani kwamitin ko-ta-kwana don tunkarar lamarin.

A wani labarin kuma, Shugaban Amurka Barack Obama ya ce za a iya samar da riga-kafin cutar Zikar nan ba da dadewa ba, idan Majalisar dokokin kasar ta hanzarta zartar da wani kudurin doka a kan hana yaduwar cutar.

Ya ce wannan abu ne da za mu iya rage hadarin kamuwa da shi idan 'yan majalisar dokoki za su dauki matakin da ya dace yanzun nan, ta hanyar ware dalolin da ake bukata don aiki da cikawa

A ranar Talatar da wuce ne masana kimiyyi a Amurka suka ce sun yi nasarar jarrabar wasu sabbin alluran riga-kafin cutar Zika a jikin Kaska, kuma za a fara jarraba su a jikin bil'adama nan ba da dadewa ba.