Mabukata sun samu tallafin Bankin Ja'iz

A Najeriya, jama'a masu hali da kungiyoyi na ci gaba da bayar da taimako ga al'ummar musulmi marasa hali a wannan lokaci na azumin watan Ramadan.

Har ma gidauniiyar taimakon al'umma ta bankin nan mai aiki da tsarin musulunci na Ja'iz da wata gidauniya ta zakka da wakafi wadda gidauniyar bankin ta kafa, suka bulla yankin kudu maso gabashin kasar, inda suka bayar da irin wannan taimako a garuruwan Nsukka da Abakaliki da kuma Umuahiya.

Mutane da dama ne dai da suka hada da maza da mata suka amfana da wannan tallafi.

Kayayyakin da aka bayar sun hadar da madara da shinkafa da ganyen shayi da kuma tumatirin gwangwani.