An kashe shugabannin IS

Hakkin mallakar hoto AFP

Amurka ta ce an halaka wasu jiga-jigan IS biyu a birnin Mosul na kasar Iraki, a wani harin da aka kai ta sama a watan Yuni.

Kakakin hukumar tsaro ta Pentagon ya ce mutanen da aka kashe sun hada da Mataimakin Ministan yakin kungiyar IS Basim Muhammad Ahmad Sultan al-Bajari, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kwace iko da birnin Mosul, shekaru biyun da suka wuce, da kuma Hatim Talib al-Hamduni, wanda babban kwamanda ne a kungiyar.

Kakakin ya ce sojojin Amurka da kawayenta sun fara fafarar mayakan IS daga wani yanki da ke kudancin Mosul.

Wakilin BBC ya ce Kakakin Pentagon ya ce mutuwar da kwamnadojin IS ke yi da kuma ruwan-wutar da ake musu ta sama a watan da ya wuce sun taimaka wajen kassara shugabancin kungiyar a Mosul.