An fara zaman makoki a Bangladesh

Hakkin mallakar hoto AP

An fara zaman makokin kwana biyu a kasar Bangladesh, bayan harin da aka kai kan wani gidan shayi a Dhaka, babban birnin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Mutum 20 aka kashe daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, kuma galibinsu 'yan kasashen waje.

Kazalika an kashe wasu 'yan sanda biyu tun ranar Juma'a, wato lokacin da aka fara kai harin.

Sojojin kundumbalar kasar ne abka gidan shayin, inda suka kashe maharan su shida, suka kuma ceci mutum 13.

Kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin.