FBI ta yi wa Hillary Clinton tambayoyi

Hakkin mallakar hoto Getty

Hillary Clinton, wadda jam'iyyar Democrat ke shirin tsaidawa takarar shugabancin Amurka a wannan watan, ta amsa tambayoyi daga hukumar bincike ta FBI, a kan yadda ta rika yin amfani da kafofin musayar email din kanta sa'adda take sakatariyar harkokin wajen kasar.

Misis Clinton dai ta ce ba ta yi wani laifi ba, ta yi amfani da kafofin ne don hakan yafi sauki.

Amma abokan hamayyarta sun ce abin da ta yin ka iya fallasa sirrin gwamnati.

Masana harkokin shari'a sun ce da wuya Misis Clinton to fuskaci shari'a kan batun, amma wani wakilin BBC ya ce tambayoyin sun zo mata a lokaci marar dadi, tun ya rage makonni kadan ne a yi babban taron jam'iyyar ta Democrat.

Karin bayani