Faransa: An bude masallaci bayan turjiyar shekara15

An bude wani masallaci a birnin Nice da ke kudancin Faransa, bayan mahukuntan yankin sun shafe shekara 15 suna adawa da bude masallacin.

Jami'in da ke kula da yankin ne ya amince da bude masallacin, bayan magajin gari, Philippe Pradal ya yi turjiya.

Shi ma magajin garin da ya gabace Philippe Pradal, wato Christian Estrosi ya yi adawa da masallacin sakamakon zargin da yake cewa wanda ya gina masallacin, wato Ministan harkokin wajen Saudiyya, Sheikh Saleh bin Abdulaziz yana kokari ne ya taimaka wajen kafa shari'ar musulunci, tare da murkushe dukkan coci-coci a kasar Saudiyyar.

Wata kotu ce ta yanke hukuncin da ya bayar da damar bude masallacin, wadda ta ce adawar da mahukunta ke yi da bude shi ya saba da 'yancin da kundin tsarin mulkin kasar ya bayar na bin addinin da ya kwanta wa kowa a rai.