Masu galihu ne suka kai harin Bangladesh

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumomi a Bangladesh sun ce sojin-sa-kan da suka kai hari mafi muni a kasar 'ya 'yan masu kudi ne kuma suna da ilmi sosai.

Ministan harkokin cikin gidan kasar, Asaduzzaman Khan, ya ce dukkan su 'yan Bangladesh ne kuma kungiyoyin da suka ingiza sun 'yan kasar ne.

'Yan sanda sun fitar da hotunan gawarwakinsu da kuma sunayensu.

Daya daga cikin wadanda suka kai harin an kama shi da ransa, kuma hukumomi na yi masa tambayoyi.

Kungiyar IS ta ce ita ce ta kitsa kai harin, wanda aka kai gidan shan shayi a Dhaka, babban birnin kasar, a ranar Juma'a.

An kashe mutane 20 a harin, wadanda yawancinsu 'yan kasashen waje ne, musamman ma 'yan Italiya.

Ana zaman makoki na kwanaki biyu yanzu a kasar.