An dakile hare-haren IS a Kuwait

Hakkin mallakar hoto Getty

Mahukunta a Kuwait sun ce sun yi nasarar dakile hare-haren kungiyar IS har sau uku, ciki har da aniyar tayar da bam a wani masallacin mabiya akidar Shi'a.

Ministan harkokin cikin gidan kasar ya ce jami'an tsaro sun kai samame a wasu wurare uku a ciki da kuma wajen kasar, kuma sun cafke wasu da suke zargi, kuma daga cikin wadanda aka kama dan sanda ne.

A bara ne, wani dan kunar-bakin-wake dan asalin Saudiya ya tarwatsa kansa a wani masallacin Shi'a a Kuwaitin, inda ya halaka mutum 27.