Ambaliya ta ci kauyuka a Pakistan da India

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane na cikin halin ha'u'la'i sakamakon ambaliyar

Wata ambaliyar ruwan sama mai karfi ta jawo asarar rayuka fiye da 30 a arewacin Pakistan.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta ce, ambaliyar ta yi awaon gaba da wani masallaci da dukkan wadanda suke cikinsa a lokacin, a kauyen Ursoon da ke gundumar Chitral.

Kazalika ba a san inda wasu dakarun tsaro takwas suke ba bayan da ruwa ya tafi da sansaninsu.

A arewacin Indiya ma a kalla mutane 25 ne suka mutu, gommai kuma suka bata bayan da ruwan sama mai yawa ya jawo zaizayar kasa da ambaliya a jihohin Uttarakhand da Arunchal Pradesh.

Ruwa ya ci kauyuka da dama ya kuma tare manyan hanyoyi, sannan kuma yawan ruwan yana kawo tsaiko wajen aikin ceto.