Hari a ofishin Amurka da ke Saudiyya

Wani dan kunar-bakin-wake ya tarwatsa kansa a kusa da ofishin jakadanci Amurka da ke Jeddah a kasar Saudiyya.

Rahotanni na cewa kunar-bakin-waken ne kadai ya mutu, ko da yake wata ruwayar na cewa wasu masu gadi mutum biyu sun jikkata.

Harin ya zo ne sa'o'i kadan kafin ranar samun 'yancin Amurka, kuma gabanin fitowar alfijir.

Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Amurka ta ce ta samu labarin harin, inda ta kara da cewa duk ma'aikatanta na ofishin jakadancin babu abinda ya same su.

Mutum 10 ne suka mutu a wani hari da aka taba kai wa ofishin jakadanci Amurka da ke Jiddan a shekara ta 2004.