'Ku daina sa kayan gargajiya a kasashen waje'

Image caption An san Larabawa da al'adar sa doguwar jallabiya da kwarkwar

Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, ta gargadi 'yan kasarta da su daina saka kayan gargajiyarsu a lokacin da suka je wasu kasashen.

Kasar ta yi wannan gargadi ne bayan da 'yan sanda a jihar Ohio ta Amurka, suka tumurmusa wani dan kasuwa a kasa kana suka tsare shi, saboda yana sanye da farar jallabiya da rawanin kwarkwar irin na Larabawa.

Wani ma'aikacin otal ne ya shaida wa 'yan sandan cewa yana zargin mutumin na da alaka da 'yan ta'adda.

Haka kuma ma'aikatar harkokin wajen kasar UAE, ta gargadi mata da su daina sanya nikabi na rufe fuska idan suka je kasashen Turawa da aka haramta irin wannan shigar.