Barclays ya fito da sabuwar manhaja

Bankin Barclays Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barclays na kokarin inganta dangantaka tsakanin sa da abokan huldar sa.

Bankin Barclays ya kara inganta manjahar sa wayar Andriod, domin baiwa abokan huldarsa da ke Birtaniya biyan kudaden sayayyar da suka yi ta wayoyin salular su.

Bankin na kokarin inganta tsarin biyan kudi da ake amfani da ita ta Google.

Dukkan biyun dai na bada damar biyan sama da Pan 100 ta wayar salula, duk da cewa idan za a biya kudin da suka kai sama da Pan 30 za a bukaci abokin hulda ya sanya lambobin sa na sirri.

Harwayau, Barclays ya ce sabon tsarin zai baiwa abokan huldarsa damar ci gaba da kashe kudaden su, ko da kuwa katin su na daukar kudi ya bata.

Hakan ya biyu bayan cewa, ko da katin ya bata, nan da nan Barclays zai samarwa abokin huldar sa sabon katin wanda zai zuba dukkan lambobin sirri da abubuwan da ake bukata a sabutar manhajar da ke wayar Android matukar an taba amfani da katin ta manhajar.

Wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum ya ce a kokarin inganta dandantaka tsakanin sabuwar manhajar ta Android da abokan hulda, za a bari a biya kudin sayayya ba tare da an bukaci dukkan bayanan da ke jikin katin abokin hulda ba.