An ba da belin Nenadi da Kayode kan N500m

Hakkin mallakar hoto AS Aruwa
Image caption Kotun ta umarci Nenadi da Mista Kayode su biya tarar naira miliyan 500

Alkalin wata babbar kotun tarayya da ke jihar Lagos a kudancin Najeriya, ya bayar da belin tsofaffin manyan jami'an yakin neman zaben Goodluck Jonathan, Nenadi Usman da Femi Fani-Kayode, kan kudi naira miliyan 500.

Alkali M.S Hassan ya amince da bayar da belin nasu ne idan har kowannesu ya biya naira miliyan 250, sannan kuma su gabatar da mutane biyu-biyu da za su tsaya musu, wadanda suka mallaki kadarori kamar yadda doka ta tanada.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 19 da 20 da kuma 21 ga watan Oktoba.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ce ta gurfanar da su a kotun, tana zarginsu da karkatar da kudin gwamnati kimanin naira biliyan biyar wajen yin harkokin siyasa.

Amma sun musanta zargin da ake yi musu, abin da yasa kotun ta bayar da umarnin rufe su.

Nenadi Usman da Femi Fani-Kayode dai sun taka rawa wajen yakin neman zaben tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan a shekarar 2015.