Mawuyacin halin da zawarawa ke ciki

Image caption Hajiya Chinyere ’yar asalin jihar Abiya na cikin tsaka mai wuya saboda shigarta musulunci da kuma mutuwar miji

A yankin Kudu-maso-gabashin Najeriya, mutuwar miji ta kan zo wa mata da dama da kalubale iri-iri, galibi a kan nuna masu tsangwama, da mayar da su saniyar ware, da cinye gadon da mazajensu suka bari.

To, sai dai da alama, a yanzu imani da wani addini shi ma ya shiga sahun matsalolin da matan yankin da dama suke fuskanta, har su auka cikin halin ni-'ya-su, idan mazajensu suka rasu.

Daga Enugu, AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya aiko mana wannan rahoton, inda ya tattauna da wata Inyamura 'yar asalin jihar Abia da ta musulunta, take kuma fuskantar irin wannan kalubale:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti