An rufe shafin Twitter na Niger Delta Avengers

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Niger Delta Avengers ta sha alwashin durkusar da tattalin arzikin Najeriya

Kamfanin sada zumunta na Twitter ya rufe shafin Twitter na kungiyar tsagerun yankin Naija Delta, wato Niger Delta Avengers.

Kungiyar dai na kai hare-hare a kan bututan man fetur na Najeriya, lamarin da ya sa kasar ta yi asarar biliyoyin naira.

Sau da dama kungiyar tana amfani da shafinta na Twitter domin sanar da jama'a hare-haren da ta kai da kuma wadanda take shirin kai wa.

Sai dai yanzu idan mutum ya yi kokarin ziyartar shafin ba zai bude ba.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato kakakin kamfanin Twitter yana tabbatar da rufe shafin na tsagerun yankin na Naija delta.

Sai dai bai bayyana dalilin rufe shafin ba, kodayake ya kara da cewa daya daga cikin sharudan yin amfani da shafinsu shi ne gujewa tayar da hankula irin na ta'addanci.