Mutum 15 ne suka mutu a harin Zamfara

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army

Akalla mutum 15 ne aka tabbatar sun mutu a wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai a kauyen Ruwan-mesa da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya.

Wani mutum da ya tsira daga harin, wanda aka kai ranar Lahadi da daddare, ya shaida wa BBC cewa maharan sun yi ta harbin kan mai-uwa-da-wabi a lokacin da mutane ke shirin yin bada-baki.

Kakakin 'yansanda a jihar Zamfara SP Sanusi Amiru ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma mutuwar mutum 15.

Mutane da dama sun samu raunukan harbin bindiga.

Rahotanni na cewa wata tawagar hadin gwiwar sojoji da mayakan sa-kai sun yi nasarar fatattakar maharan da ake jin 'yan fashin shanu ne.

Jihar ta Zamfara dai na shan fama da hare-haren mutanen da ake zargi barayin shanu ne.

Ko da a kwanakin baya sai da wani tsohon dan majalisar dattawa daga yankin, Sanata Sa'idu Dan Sadau ya bukaci gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta-baci a jihar.