Masallacin tafi-da-gidanka a Indonesia

Hakkin mallakar hoto AP

A duk lokacin da aka yi kiran sallah a Jakarta babban birnin Indonesiya, Sutikno, wani musulmi mai tsantseni, yana kokarin ganin ya dauko matarsa a kan lokaci ba tare da cunkoson motocin birnin ya hana shi samun jam'i ba.

Amma sai gashi cikin sauki an samo mafita ga mutane irinsa da basa son kwaramniyar yau da kullum ta hana su yin ibadarsu a kan lokaci.

An samar da masallacin tafi-da-gidanka a birnin na Jakarta cikin watan Yuni, daf da kusantowar watan Ramadan, domin a taimakawa mutane wajen ganin basu rasa yin sallah a kan lokaci ba.

An ajiye irin wadannan masallatai na tafi-da-gidanka a wuraren da jama'a suka fi yin kai-kawo.

Sutikno, matashin ma'aikacin gwamnati ne, ya kuma ji matukar dadi a lokacin da ya ga wata mota irin ta daukar kaya, wadda da irinta ake masallacin tafi-da-gidanka din, an ajiyeta tsakanin wani filin wasanni da rukunin shaguna.

Ya ce, ''Da hanzari nake na je wani masallaci da na sani mai nisa daga inda nake, amma kwatsam sai na ci karo da wannan na tafi-da-gidanka din.''

''Sai kawai na ajiye motata a gefe, na shiga waccar motar na yi sallah. Hakan ya taimaka min wajen zuwa daukar matata a kan lokaci ba tare da sallar ta kubuce min ba,'' in ji Sutikno.

'Yadda masallacin ke amfani'

Motar mai launin fari da kore ta zamo wani wajen gabatar da ibada.

Idan lokacin salla ya yi, sai a bude kofofinta, kuma akwai Liman da ke yin wa'azi.

An shimfida darduman salla a cikinta, kuma tana da filin da ke daukar a kalla mutum 100 da za su iya ibada a ciki.

An kuma samar da tankin ruwa saboda masu bukatar alwala da kuma hijaban salla ga mata.

Hakkin mallakar hoto REUTERS

An fara wannan masallaci ne da tawagogi hudu a cikin watan Ramadan, amma ana shirin cigaba da amfani da su har a bayan watan azumin.

Motar na fara aiki ne daga karfe uku zuwa bawai na yamma, a lokacin da cunkoson ababen hawa ke ta'azzara a birnin, inda dubban mutane ke makalewa har su rasa salla a kan lokaci.

Haka kuma, a lokacin azumin, masu kula da masallacin kan rarraba abin makulashe ga mutanen da suka makale a cunkoso a lokacin bude baki.

'Kungiyar da ta samar da masallacin'

Cibiyar Masallaci ta Archipelago ta samar da motocin. Wata kungiya ce da ke gina tare da tafiyar da masallatai inda wata kungiya ta Adira Sharia ke samar da kudaden da ake amfani da su don sayen ababen hawar.

Daraktan cibiyar Hamzah Fatdri, ya ce, ''Mun damu kwarai kan rashin isassun wurin ibada a wuraren da aka fi samun cunkoson mutane da abin hawa.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akwai masallatai kusan dubu 800 a Indonesiya

Ya kara da cewa, ''Wani lokacin mutane na son su yi salla, amma rashin wajen da za su yi ta cikin nutsuwa sai yasa su dinga tsallaketa.''

Kasancewar Indonesiya kasar da al'ummar musulmai suka fi yawa, yasa suke da yawan masallatan da suka kai dubu 800.